![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/08/FB_IMG_1660077990742.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
Bidiyon Kama Wata Mai Safarar Yara A Maiduguri, Inda Ta Kwashi Yara Uku Za Ta Kai Su Jihar Lagos
An kama wannan mata mai suna Nsa Heneswa a tashar Borno Express dake Maiduguri yayin da take kokarin tafiya jihar Lagos da yara uku da ta sace.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/08/FB_IMG_1660075922298.jpg?resize=300%2C225&ssl=1)
A bayanin da ta yi tace dubu dari biyar Lady B dake Victoria island a Lagos ta biya ta domin ta yi wannan aikin.
Kuma wannan ne karon farko da ta yi nasarar samun yara, sannan kuma ta ce akwai wata nurse a Maiduguri Specialist Hospital da take taimaka mata akan wannan aika-aikan.
Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu Allah ka zaunar da kasar mu lafiya.
Daga Yahaya Yakubu Alasan Barbaji