Kannywood News

Jarumi Ali Nuhu Ya Nuna Takaicinsa Akan Abinda Ya Faru A Jahar Oyo

Fitaccen jarumin shirya fina finan hausa a kannywood Ali Nuhu yayi Allah wadai da kisan mutane a jahar oyo.

Jarumi Ali nuhu ya bayyana takaicin nasa a shafinsa na sada zumunta tare da yin Allah Wadai da wannan aika aikar.

Wallafar Jarumin A Shafinsa Na Sada Zumunta.

Jarumin ya bayyana cewa. Kashe rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba da lalata dukiyoyi a Ibadan abin takaici ne, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi abin da ya kamata, hotunan da bidiyon da ake yadawa Abin damuwa ne.

StopTheBlood Adaina zubar da jini ibadanCrisis

Jarumi Ali Nuhu Tare Da Abba Elmustapha.

Tun bayan faruwar Wannan lamari jarumai da dama daga masana’antar ta kannywood ke Allah wadai da wannan aika aikar.

 

Sarki Ali Nuh.

Ciki kuwa hadda jaruma rahama sadau da jarumi Abba elmustapha dakuma falalu a dorayi da dai sauran su.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button