News

Yarabawa sun fara kokawa da tsadar kayayyaki A Garin Oyo inda akai rigama da hausawa


Yarabawa Sun Fara Kokawa Da Tsadar Kayayyakin Masarufi A Garin Oyo Inda Akai Fada Da Hausawa

Rahotanni daga jahar oyo na bayyana cewa kayayyakin masarufi sunfara yin tashin gwauron zabi tare da wahalar samu a jahar.

Tun bayan faruwar wani rikici tsakanin hausawa mazauna jahar oyo dakuma yarabawa a wata kasuwa da ake kira shasha market. lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi tare da jikkata daruruwan mutane wanda galibin su hausawa ne da suka fito daga yankin arewacin kasar.

Kasuwar Shasha inda tarzomar ta tashi.

Tuni dai Wasu kungiyoyi suka fara Yin  kiraye kiraye ga yan Arewa. Da su kauracewa siyan kayyaki ko siyarwa ga  yan kudu. kamar yadda kungiyar marubutan Arewa mai suna Arewa Media Writteres. Sukai kira da’a kauracewa Siyan kayayyakin yarabawa da duk wasu nau’in kayayyaki da’ake shigowa dasu daga kudu. Domin nuna rashin jin dadin abinda ya faru da hausawa yan arewa dake rayuwa a oyo.
Wallafar Arewa Media Writters A Shafinsu Na Facebook.

Haka zalika an cigaba da kiraye kiraye ga yan Arewa dake kai kayan Abinci da na masarufi kudancin kasar da suma su dakata domin yin hakan kan iya sawa su fahimci cewa lallai hausawa nada girman da bai dace a wulakanta su hakaba.

Jim kadan bayan wannan kiraye kiraye rahotanni sun fara bayyana cewa. Tabbas wannan kiraye kiraye da akai dakuma amsawa kiran da wasu yan kasuwar sukayi na kin kai kayan abinci da na masa rufi kudu. Yayi amfani matuka.

 

Inda rahoton ya bayyana cewa yanzu haka farashin kayayyaki yayi tashin gwauran zabi tare da wahalar samu a kudu musamman ma jahar ta oyo inda anan rikicin ya faru.

Related Articles

2 Comments

  1. Agaskiya muma anan jihar ondo State haka abinyake wajen tashin kayan abinci kuma muna rokon allah yasa bayanzu za,akoma saisinji ajikinsu tukunna allah yataimaki AREWA da al umman AREWA baki daya daga adam kabir beli Kano State

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button