Kannywood News

Daraktocin Kannywood Sunyi Magana Kan Batun Kama Dan Hisbah Da Matar Aure.


Manyan Daraktocin Kannywood Sun Koka Kan Yadda Ba’a Yayata Dan Hisban Da Yai Lalata Da Matar Aure ba.

A Jiya Muka Kawo Muku Labarin Dan Hisban Da Aka Kama Da Laifin Lalata Matar aure Dudumu A Dakin Hotal. Wanda Mijinta Ya Shigar Da Korafi Aka Bi diddigi har Takai Ga Ankamasa Dumudumu har dakin da yakama Yakai matar Aure A Unguwar sabon gari.

Jami’in Hisbah Da’ake Zargi Da Yin Lalata Da Matar Aure A Hotal.

Sai dai wasu manyan daraktocin kannywood sun koka kan yadda aketa lullube labarin. A cewarsu da dan film ne da tuni duniya ta dauka da malamai masu wa’azi. amma da yake ba dan film bane shiru kake ji.

Dafari Dai Darqkta hassan gigs ne ya fara wallafa cewa.
Allah Sarki da dan film ne da tuni labari ya chanza Allah ka shirye mu gaba ki daya amin. Matar aure fa hmm.

Wallafar Daraktan A Shafinsa Na Instagram.

Inda ya kara da cewa a duniya munafurci yayi yawa a ko ina shiru kakeji Allah ka iya mana badan halin mu ba. Wannan shafi nane in kai maganar banza in gimtseka.

Kana Dayan Abokin aikinsa Sadik m. Mafiya kamar sun hada baki. Shikuma ya wallafa cewa.

Daga hmm sai uhmm Amma Da Dan Kannywood Aka Kama Yau Da Tuni Shehunnan Facebook Sun cika ko ina da tsinuwa ga Yan Film.

Daraktan Ya Wallafa Hakan ne a shafinsa na Facebook.
Darakta Sadik M. mafiya.

Sai dai a wani gefen ana cigaba da bayyana ra’ayoyi kan wannan lamari , inda daukacin masu tsokacin kan wannan batun musamman ma a shafukam Facebook ke kira idan an tabbatar da laifin nasa a yanke masa hukunci irin wannan shari’ar musulimci tazo dashi domin zama misali ga Alumma tunda sune sojojin musulimci masu hani ga laifi kuma aka sami wani a cikinsu ya aikata zaifi kyau a buga misali dashi wajen tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro

Tuni dai kwamandan hisbah ya kafa kwamatin bincike dan gudanar da bincike dakuma gabatar masa da sakamakon binciken cikin kwanaki uku

Darakta Hassan Giggs Da Abokinsa.

Dafatan Allah Yasa Mufi karfin zuciyar mu yakuma kare mu daga sharrin shaitan Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button