Yadda Kayayyakin Abinci Ke qara Tsada A Kudancin Nigeria Sakamakon Kin Shigar Da Kayan Da Yan Arewa Suka Daina.

Lamarin dai ya faru ne biyo bayan wani rikici da ya barke a wata kasuwa dake jahar oyo wanda yai sanadiyar salwantar rayuwaka dakuma dimbin dukiya.
Rikicin dai yafi shafar hausawan kasuwar dakuma wasu dake zaune a cikin jahar oyo.
Hausawa na zargin manyan yarabawa da iza wutar rikicin tare da nuna halin ko in kula da cin kashin da ake musu.
Dankalin Da Ake Kaiwa Kudu Daga Yankin Arewa
Shugabannin yan kasuwa Daga Arewa sun fusata gami da shiga yajin aikin dena kai kayan abinci kudu har sai an biya diiyan wadanda aka kashe tare da biyan su kudaden da sukayi asara.
Rahotanni na bayyana cewa kwana biyu da fara wannan yajin aikin dena kai kayan abinci kudu.
Kasuwar Tumatur Da Hausawa Ke Kaiwa Kudu Daga Arewa
Hakan tasa yan kudun ke kokawa tare da fuskantar siyan kayan abinci da tsadar gaske a garin.
Ku bayyana mana ra’ayoyinku Kuna goyan bayan wannan yajin aikin? Ko kuma hakan bai dace ba?

Click Here To Drop Your Comment