Tun biyo bayan rikicin kabilanci a kudancin nigeria wanda yai sanadiyar mutuwar hausawa fiye da dari tare da asarar dimbin dukiyar hausawa fataken abinci.

Shugabannin kungiyar hausawa masu safarar abinci izuwa kudu suka umarci mambobin su da su dakata da kai kayan abinci kudancin nigeria har sai gwamnati ta dauki mataki akan kisan gilla da cin kashin da ake musu tare sa biyan fansar asarar da sukai.

Lamarin da yakai ga assasa hauhawar farashin kayan masarufi a yankin kudancin nigeria .

Kasuwar Mayanka Inda Ake Saida Naman Shanun Da Yan Arewa Suka Kai Kudu.

Wanda kuma kullum abin qara sama yakeyi tare da barazanar qara jefa yankin na kudu cin qangin talauci.

A wani rahoto da jaridar madubi- H suka fitar a shafin su na Facebook Sun bayyana cewa.

Alummar yankin kudu na rokon yan arewa fataken abinci da suwa Allah Su Yafe Musu tare da janye wannan yajin aikin.

Su cigaba da kawo musu kayan abincin Inda Suka Alwashin hakan bazai sake faruwa ba.

Kasuwar Kayan Miya Inda Ake Saida Kayan Miyan Da Yan Arewa Suka Kai Kudu.

Sai dai mutane da dama na bayyana ra’ayoyin su akai yayinda suka ke cewa ko za’ai musu afuwar to a bari su ji a jikinsu tukunna.

A gefe guda kuma waau ke ganin tunda sun gane kuren su harma sun fto da kansu sun nemi yafiya to a yafe musu kawai zaifi.

Anan mukeso da ku bayyana mana ra’ayoyinku. Shin yakamata a janye wannan yajin aikin haka? Ko kuma aci gaba har sai gwamnati ta dauki matakan da suka dace tare da biyan yan arewa diyyan asarar da sukayi?

Click Here To Drop Your Comment