Uncategorized

Bayan Zagi Da Tasha Saboda Yin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Sayyidina Ali Farin Jinin Ta Ya Sake Nin Kuwa

Farin Jinin Jarumar Kannywood Aisha Abdurra’uf Ya Karu Albarkar Sayyiduna Ali AS.

Tun bayan wata wallafa da jarumar kannywood Aisha Abdurrauf wadda akafi sani da Aisha Izzar So, Tayi a shafinta na Instagram da nufin taya yan uwa musulmai murna da zagayowar ranar haihuwar Sayyiduna Ali A.S.

Dayawa daga cikin mabiya shafin na jarumar suka dinga bayyana ra’ayinsu akai.

Yayinda wasu ke tayata murna da hakan a gefe guda kuma wasu na zagi da cin mutumcin jarumar gami da zarginta da zama yar shi’a

Lamarin dai baiyiwa jarumar dadi ba inda ta fito a karo na biyu cikin wani sabon bidiyon da ta sake wallafawa a shafinta nata na Instagram tare da yin wasu tambayoyi.

Lokacin Da Ta Sake Dawowa Cikin Wani Bidiyon Tana Yin Martani Ga Masu Zagin Nata.

Bidiyon dai ya shahara a shafukan sada zumunta inda jama’a suka dinga yabawa jarumar gami da jinjina.

Tare da kara baiwa jarumar kwarin gwiwar cigaba da nuna soyayya ga Ahlul baiti batare da jin tsoron mai zargi ba.

Yayinda a Gefe guda kuma manyan malamai suka dinga yin tambihi akan wannan bidiyon.

Wanda sai da takai ga an tattauna da manyan malumma daga bangaren izala dakuma tijjaniya akan wannan Bidiyon na jarumar dakuma zagin da wasu suka dinga yiwa jarumar akan nuna soyayyar ta ga imam Ali.

Jaruma Aisha Izzar So

Wanda Ko A Daren jiya munga sanarwa a babban shafin Sarki Zaki Dake Facebook inda suka sanar da tattauna batun tare da sheikh Musa Yusif Ahsadusunnah

Baya da haka binciken mu ya gano yadda jarumar da dinga shan yabo dakuma kara samun masoya.

Wanda mafi akasarin mutane ke bayyana soyayyar su ga jarumar tare da ayyana cewa daga yau sun shige jerin masoyanta saboda son da takewa sirikin Annabi.

Anan mukeso da ku bayyana mana ra’ayoyinku?

Shin Yan Shi’a kasai Ne Yakamata Su so Ahlul Baiti?

Related Articles

3 Comments

  1. Shi dama imam Ali (a.s) ba Mai sonsa sai mumini Kuma ba Mai kinda sai munafiki. Dan haka duk cikar masoyansa Babu munafiki.

  2. Nima a wannan abun da tayi yasa na shiga cikin masoyanta, ban Taba ganin film din izzarso ba,Amma saboda ita yanxu Zan Fara kallonsu tun daga farkon Har zuwa episode din da aka tsaya, sannan kuma wajibine Ga Duk musulmi mumini da yayi imani da annabi s.a.w yaso sayyadi Aliyu in bahaka ba to munafuki Allah ya tsaremu da nifaqa Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button