Farashin kayan Abinci yayi mummunan tashin da bai tabayi ba a kudan cin Nigeria.

Alummar kudancin nigeria na cigaba da kokawa kan yadda yan Arewa suka hada kai kan qin shigar musu da kayayyakin abinci.

Lamarin da ya jawo hauhawar farashin kayayyakin abincin da suka rage a yankin.

Wanda muddin Yan Arewa basu dakatar da yajin aikin da suka soma na qin kai musu kayan abinci su saya ba Hakan Ka iya shafar kasuwanci dama karya kana nan yan kasuwa.

Jama’a da dama daga yankin na rokon Shugabannin yan kasuwar da suwa Allah su dakatar da yajin aikin nan haka.

A ta bakin shugaban Yan kasuwar safarar kayan abinci ta kasa Dr.Muhammad Tahir. Cewa Yai Muddin ba’a biya su Asarar da sukai ba dakuma diyyar mutanen da aka kashe musu tun daga lokacin fara zanga zangar kawo karshen rundunar yan sandan Sars har izuwa yanzu to kar ma asaka rai da janye yajin aikin da suka soma.

Lamarin da wasu ke ganin ya dace ace sun tsagaita da wannan yajin aikin domin yan kudu su sami saukin tsadar rayuwa.

A inda wasu ke ganin abar yan kudun suma su dan dana kudar su. Ko zasu gane amfanin hausawa a gare su.

Anan muke so daku bayyana mana ra’ayoyin ku kan wannan batun.

Shin kuna goyan bayan kungiyar masu kayan abinci ta Arewa ta janye yajin aikin nan ko kuwa aci gaba

Click Here To Drop Your Comment