Kasuwanci A Kudu Ya Fara Durkushewa Saboda Yajin Aikin Masu Kayan Gwari Daga Arewa.

Tun rikicin kabilanci da ya faru a kudancin Nigeria wanda yai sanadiyar rasa rayukan wasu yan kasuwa dakuma Asarar dimbin dukiya.

Shugabannin Yan kasuwar gwari dakuma na kayan Abinci dama na dabbobi suka tsunduma yajin aikin daina kai kayan Abinci kudu saboda nuna muhimmancin su ga yankin.

Dakuma nuna bacin ransu kan yadda ake nuna musu tsana da wariya dakuma kiransu cima zaune.

Tun fara yajin aikin izuwa yanzu dai lamura suketa chanzawa farashi yaketa hauhawa kasuwanci yaketa durkushewa lamarin da ya tilasta mutanen yankin kudun rokon yafiya ga yan Arewa da suwa Allah su janye yajin aikin.

 

Kamar yadda mutane da dama keta tofa Albarkacin bakinsu game da wannan yajin aikin a shafukan sada zumunta. Wasu na ganin yakamata yan Arewa su dakatar da yajin aikin haka.

A gefe guda kuma wasu ke cewa Acigaba da yajin aikin har sai yan kudun sun shigo Arewa dakan su sun sayi kayan Abincin

Click Here To Drop Your Comment