News

Yadda Ragon Dubu Goma Sha Biyar A Arewa Yakoma Naira Miliyan Daya A Kudu. Saboda Yajin Aikin Yan Arewa

Hauhawar Farashin Kayayyakin Abinci Dakuma Dabbobi Da Kayan Gwari Da Ake Kaiwa Yankin Kudancin Nigeria Daga Arewa Na Cigaba Da Ci Kamar Wutar Daji A Yankin.

Tun bayan wani fadan kabilanci da ya faru a kudancin nigeria a garin oyo Wanda yai sanadiyar rasa rayukan wasu hausawan dake saida kayan abinci a yankin dakuma Dukiyar Su masu tarin yawa.

Lokacin Da Akaiwa Yan Arewa Asarar Rayuka Da Dukiyoyi

Lamarin dai baiyiwa kowanne dan Arewa dadi ba. Wanda hakan ya fusata kungiyoyin Yan Arewa da Dama musamman Ma na shafukan sada zumunta.

Wanda dalilin hakan yasa akaita kiraye kiraye ga yan Arewa mazauna kudu. da su tattara inasu inasu su bar musu yankin su ko dan Samun tsira da rai da mutumci.

Lamarin da masu kirayen ke zargin kallon cima zaune kawai yan kudu kewa Alummar Arewa. Don Kawai Suna ganin ana hako man fetur daga yankin su.

Jim kadan bayan wannan kiranyen ne kawai sai ji akai Shuwagabannin kungiyar fataucin kayan Abinci ta kasa musamman ma yan Arewa Sun tafi yajin aikin daina kai Kayan Abinci kudu.

Lamarin da acikin kwana biyu kacal ya fara Rikita tunanin su tare da fara sanin cewa lallai Yan Arewa ba cima zaune bane. kamar yadda wasu jagororinsu ke Yaudarar su Cewa ai yan arewa cima zaune ne basu da komai sai dai a hako man fetur daga yankin su a sayar a rabawa yan Arewa kudin.

Haka abu yai ta faruwa a kudu farashi yaita hauhawa wanda hakan ke baraza ga karyewar kana nan yan kasuwar dake yankin kudancin.

Kamar yadda wasu rahotanni suke bayyana cewa rashin rago yayi tashin gwauran zabi in yanzu haka ake sayarda rago dubu dari takwas dubu dari tara har zuwa miliyan daya.

Yayin farashin shanu kan fara daga miliyan biyu zuwa sama.

Farashin kaji kuma kan fara ne daga dubu biyu da dari biyar zuwa sama.

Farashin kayan miya kuwa ba’a cewa komai domin. Domin A wani wajen tumatir kwalli daya yana kaiwa har dari biyu.

Albasa kuwa duk daya kan fara daga dari biyar ne zuwa sama.

Tabbas wannan yajin aikin yayi matukar daga daraja dakuma fito da amfanin yan Arewa musamman hausa fulani a nigeria.

Wanda hakan ke nuni da cewa idan muka dogara da noma kadai to bawani wanda zai yi mana gorin man fetur.

Allah ya taimaki Arewa da yankin Arewa Amin Summa Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button