News

Yan Kudu Sunji Kunya Bayan Da Aka Gano Wani Hoton Karya Da Suke Yadawa

Yan Kudu Sunji Kunya Bayan Da Aka Gano Gaskiyar Wani Hoto Da Suke Yadawa A Kafafan Sada Zumunta.

Inda Acikin Hoton Akaga Shanu Na Cin Wani Tumatir Mai Yawan Gaske. Inda Yan Kudu Suke Yada Cewa Yan Arewa Ne Suka Tafka Asara Bayan Yajin Aikin Daina Kai Kayan Abinci Kudu.

Irin Yadda Suke Yada Labarin Karya Game Da Asarar.

Kamar yadda jaridar HumAngel ta rawaito cewa Hoton Shanun da aka gani suna cin tumatir ba’a nigeria bane. kamar yadda wasu ke yada jita jitar cewa lamarin ya faru a Arewacin Nigeria ne bayan yajin aikin da masu kayan abinci na Arewa suka shiga na daina shigar da kayan Abinci kudu.

Haka Zalika HumAngel ta rawaito cewa hoton an dauke shi ne a kasar india. Ba’a Arewacin Nigeria ba.

Tun bayan yajin aikin da yan kungiyar fataken kayan abinci ta kasa suka shiga na daina kai kayan abinci kudu.

Biyo bayan wani rikici da ya faru a jahar oyo lamarin da yakai ga asarar rayuka dakuma dukiya mai dimbin yawa.

Lamarin tafiya yajin aikin daina kai kayan Abincin kudu ya dauki hankali kwarai dagaske inda yakumasa farashin kayayyaki a kudu sukai tashin gwauron zabi.

Wanda hakan ya janyo musayar yawu tsakanin yan kudu da yan Arewa. Inda yan Arewa ke ganin tafiya yajin aikin da masu kayan abinci sukai yayi matukar tasiri domin yan kudu naji a jikin su.

Yayin da yan kudun ke cewa ai yan Arewa ne keji a jikinsu domin sai tafka asara suke ta kayayyakin da sukaqi kawo kudun gashi can sun ajje shanu nata ci.

Gami da yada wasu hotuna tare da shanu na cin tumatir.

A wani bincike da HumAngel ta Gudanar ta gano cewa hoton da Ake Ta Yadawa Na shanun da ke cin tumatir ba’a nigeria bane

An dauki hoton ne a kasar india kamar yadda kuke gani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button