Kannywood News

Jarumin Cikin Shirin Kwana Casain Ya Maida Martani Ga Masu Aibata Kyawun Matarsa

Abinda Ya Faru Da Sahabi Madugu Da Matarsa Hassana

A Ranar Lahadin Nan ne dai aka daura auren jarumin tare da matarsa hassana

Sai de bayan bayyanar Hoton Auren Nasu Ne a Shafukan Sada Zumunta Mutane da dama suka dinga yin maganganu marasa Kyau Game Amaryar Tasa Harma Wasu Ke Cewa Ai Yama Fita Kyau Aji Da Dai Sauran Su

Bayan Wadannan Maganganu da makamantan su sunyi Yawa a duk inda Aka Wallafa Hotunan Auren Nasu.

Lamarin da Yasa sahabin fitowa tare da yin tsokaci game da bayyana irin Halaccin da matar tasa hassana tai masa inda ya wallafa cewa..

SUNANA ALIYU HUSSEIN….
Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aibata halittar ta, sun san ni bayan dana zama SAHABI a cikin shirin Kwana Chasa’in, basu sanni a lokacin da nake Aliyu ba….

Alhamdulillah Hassana ta kaunaceni a lokacin da ni ba kowan kowa bane, lokacin da hatta a unguwarmu ba kowa bane yasan dani, don haka ne nima na rike alkawarin ba zan iya rabuwa da Hassana ba, koda kuwa me na zama a wannan duniyar…

Akwai Yan’mata masu yawa da suka nuna kauna gareni a yanzu bayan dana zama SAHABI, to amma anya kuwa Aliyu suke so, kodai Sahabin Kwana Chasa’in suke so…?

Soyayya ta tsakani da Allah Hassana ke yimun, haka nima dai soyayya ta gaskiya nake mata, ni da ita ba kyale kyale muka kalla ba…

Ni Aliyu Hussain ina cigaba da yiwa Allah godiya sakamakon kyautar Mata Hassana daya bani, ina kallon kyawunta kwatankwacin sarauniyar kyau ta duniya, ina addu’ar Allah ya hadani da Matata Hassana a aljana…..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button