News

Wani Inyamuri Dan Kabilar Igbo Ya Tafka Satar Motar Da Farashinta Yakai Dalar Amurka $300K

An cafke wani dan kabilar Ibo Wato Inya Muri da satar Motar Da Farashinta Yakai $300K Rolls Royce Cullinan a Amurka.

Wani dan Najeriya mai shekaru 23, Mai Suna Ezonachukwu Obianefo, ya shiga hannun ’yan sanda a Houston, Texas, Amurka,

kan zargin satar wata Rolls-Royce Cullinan, wacce darajarta Takai Kimanin Dalar Amurka kusan $300,000.

Kamar Yadda Jaridar Conan Daily ta rahoto cewa Obianefo na tsare a gidan yari na Harris County a Houston kuma an sanya belin sa kan $ 50,000.

An tattaro cewa Obianefo shine manajan kamfanin sarrafa kayayyaki, wanda ke samar da ayyukan sufuri. A cewar ofishin babban lauyan gundumar Harris County, an ce mamallakin motar mazaunin Florida ne, Amurka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button