Kannywood News

Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale Ya Tsaya Takarar Siyasa A Jahar Kano

Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale Ya Tsaya Takarar Siyasa A Jahar Kano

Fitaccen Jarumin Shirya Fina Finan Hausa Na Kannywood Daddy Hikima Wanda Akafi Sani Da Abale.

Ya Tsunduma Harkar Siyasa, Jarumin Wanda Aka Hango Psotar Takararsa Tana Yawo A Shafukan Sada Zumunta.

Kamar Yadda Shima Da Kansa Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagram, An Hango Jarumai Da Dama Na Tayasa Fatan Alkhairi.

Jarumin Ya Wallafa Hoton Wanda Ke Nuni da cewa zai fito a mai wakiltar Kumbotso Inda Ya Wallafa Cewa,

Mulki na Allah ne yana baiwa wanda ya so a sanda ya so. Mun fito da karfin Allah tare da goyon bayan mutane don mu wakilci mutane daga cikin mutane zuwa ga mutane don mutane.

Muna nemar yardar Allah tare da rokon Allah ya sa mutane su yarda da manufofin matukar basu kauci tafarkin nagarta ba.

Allah Karka Barmu da Iyawarmu ko Wayonmu,
Allah Idan da Alkhairi Acikin Tafiyarnan Allah Ka Tabbatar dan Arzikin Manzon Allah S.A.W
#Abaleforreps
#kannywood

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button