Kannywood News

Kalli katafaren gidan da Rukayya Dawayya ta gina suka tare da Angonta Afakallahu

Kalli katafaren gidan da Rukayya Dawayya ta gina suka tare da Angonta Afakallahu

Rukayya Dawayya tana daya daga cikin tsofaffin Jaruman Kannywood da suka taka rawar gani har aka samu masana’antar ta kafu ta kai ga wannan lokacin, sanin kowa ne a satin daya gabata ne aka daura Auren ta da tsohon bazawarinta Shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano Isma’il Abba Afakallahu.

Haka kuma a watannin baya ne jarumar Dawayya ta bayyanawa duniya irin katafaren gidan da take ginawa,kwatsam kuma sai a wannan lokacin aka gano jarumar ta wallafa a shafin ta yadda aka kammala gidan har kuma suka tare da Angon nata Afakallahu a gidan.

Mutane da dama sun cika da mamaki da ganin hakan,domin wasu suna ganin wata iriyar Sana’a take da har ta kai da tatara irin kudin ginin wannan gidan na Alfarma,sai dai kusan kowa ya sani jarumar “yar Kasuwa ce ko a kwana 10n da suka gabata an ganota ta bude sabon wani sabon shagon ta na kasuwanci.

Ba tare da bata lokaci ba zamu nuna muku bidiyon gidan anan kasa,Kada ku manta kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Ga bidiyon:

https://youtu.be/7apayLSIhh0

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button