News

KU CASU: Ƴan ta’adda da dama sun mutu yayin da ƴan Boko Haram da ISWAP su ka gwabza faɗa

KU CASU: Ƴan ta’adda da dama sun mutu yayin da ƴan Boko Haram da ISWAP su ka gwabza faɗa

Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa takwarorin su na ƙungiyar ISWAP kwanton-ɓauna, inda su ka kashe mayakan da dama a wani sabon yakin neman suna a tsakanin bangarorin biyu masu tsattsauran ra’ayi.

Wani faifan bidiyo da jaridar PRNigeria ta samu, ya nuna yadda kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Buduma suka yi holon wasu mayakan ISWAP da dama, tare da yayyanka su a wata maƙabarta ta wucin gadi.

Daga baya mayakan na Boko Haram sun kona wasu ‘yan ta’addar ISWAP ɗin da ransu a cikin motocin yaki.

Bayan haka kuma, dakarun Rundunar Haɗin-gwiwa ta Ƙasa da kasa, MNJTF, a ranar Laraba sun kawar da mayakan ISWAP da ba su yi ƙasa da guda 33 ba.

An kuma jiyo cewa dakarun na MNJTF sun ceto mata da ƙananan yara da dama a wani samame da sojoji suka kai a Ƙaramar Hukumar Gamborun Ngala ta jihar Borno.

PRNigeria ta jiyo cewa kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da manyan motoci da babura da manyan makamai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button