News

LABARI MAI DADI: Za’a Cigaba Da Amsar Tsoffin Kudi Har Bayan Wa’adin Da Aka Sake Karawa.

LABARI MAI DADI: Za’a Cigaba Da Amsar Tsoffin Kudi Har Bayan Wa’adin Da Aka Sake Karawa.

Gwaman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankunan ƙasar za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun kuɗi daga hannun kwastomominsu har zuwa bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu, lokacin da za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗin a ƙasar

Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da ya hallara a gaban kwamitin wucin-gadi kan sauya fasalin kuɗin ƙasar na majalisar wakilan ƙasar.

To sai dai gwamnan babban Bankin bai bayyana lokacin da bankunan za su daina karɓar tsoffin takardun kuɗin ba.

Tun da farko dai kakakin Majalisar Wakilan ƙasar Femi Gbajabiamila, ya zargi gwamnan babban bankin da saɓa wa sashe na 20 na dokar CBN wadda a cewarsa ta wajabta wa bankunan ci gaba da karɓar tsoffin kudin har zuwa bayan wa’adin da Babban Bankin ya saka.

Yayin da yake jawabi a gaban kwamitin Emefiele, ya ce ya yarda da ‘yan majalisar game da sashe na 20 na dokar CBN.

”Sashe na 20 na cewa bayan cikar wa’adi za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗi, to amma an wajabta wa bankuna karɓar ƙuɗaɗen. Dan haka ina tare da majalisa a kan haka”, in ji Emefiele.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button