Kannywood News

Mafi Yawan Hausawa Munfi Iya Zagi Da Cin Mutunci Da Dariyar Ƙeta Ga Junanmu

Mafi Yawan Hausawa Munfi Iya Zagi Da Cin Mutunci Da Dariyar Ƙeta Ga Junanmu

Daga Abdulrahman Wadata Katsina

A lokacin da fuskar yarinyar nan ta tafara bayyana tabbas jama’a da yawa suna mata kallon mutuniyar kirki saboda wasu kyawawan ɗabi’u, da ta fito da su a cikin shirin kwana casa’in.

Bayan bayyanar videon ta na tsirai ci, Daga lokacin abubuwa suka sauya mata, musamman daga ɓangaran rayuwa da mu’amularta da jama’a, tabbas tayi kuskure ita kanta tasan haka daga baya.

A lokacin tana bukatar tausayawa da kulawa ta musamman da shawarwarin rayuwa, ko babu komai wanda ya mata nasiha zai samu ladar nasihar ba zaginta ba

Bayan hukumar da ke da hakki da finafinan hausa ta da katar da ita daga shirya fina finai musamman ma kaco kam ita kanta Arewa 24 din, a lokacin sun cire ta acikin fim ɗin saboda ƙorafe-ƙorafen da ake kawowa da kuma zahirin abinda suka gani.

Wa,iyazu billah! Wallahi tallahi naji tausan yarinyar nan matiƙa sosai, domin nasan wallahi rashin gata da mafaɗa ne ya cuci rayuwarta, dan Allah asamu wasu suyi aikin Allah wajan ceto rayuwar ‘yar nan ayi aikin Allah da na addinin Allah. Domin zagin da ake mata bakin wani zai iya jefata cikin wata masifar, saboda baasan bakin wani ba.

Tabbas barinta haka sa-ka-ka kamar ba ta da kowa abin takaici ne garemu ta fuskoki da yawa, Addininmu da al’adun mu basu bamu damar zuba ma irin hakan ido ba, matuƙar munada yadda zamuyi, Ku dubi gaba ɗaya ya nayin ta ya sauya hankalin ta ya fara barin jikinta, kamanninta sun fara komawa kamar ba ita ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button