Kannywood News

Magana ta fito fili tsakanin soyayyar Hamisu breaker da Fatima Ali Nuhu yar gidan sarki Ali Nuhu

Magana ta fito fili tsakanin soyayyar Hamisu breaker da Fatima Ali Nuhu yar gidan sarki Ali Nuhu

Idan baku mantaba tun shekarar dubu biyu da ashirin akwai rahotanni dasuke bayyana cewar mawaki hamisu breaker da Fatima Ali Nuhu suna soyayya mai karfi.

Wanda a wannan lokacin mutane sunyita tofa albarkacin bakinsu dakuma nuna jindadi ganin a wannan lokacin mawaki hamisu breaker yana tashe, sanadiyyar wakarsa maisuna (jarumar mata).

Inda a wannan lokacin mutane suna fadin cewar tabbas indai labarin haka yake kuwa to Hamisu breaker da Fatima Ali Nuhu sun dace domin kuwa hakan zai kara dankon zumunci sosai a masana’antar Kannywood.

Saidai acikin shekarar bayan bikin karamar sallah 2020, gidan jaridar BBC Hausa sunyi hira da mawaki Hamisu breaker inda acikin hirar harsuke tambayarsa menene gaskiyar Alaqar sa ta soyayya da yar gidan Ali Nuhu wato fatima Ali Nuhu.

Hamisu breaker ya bayyana cewar shi babu wata soyayya tsakaninsa da ita hasalima rabonda ya ganta tun tana yar karama wannan labarin da mutane suke wallafawa duk labarin karyane shi babu wata soyayya tsakaninsa da fatima Ali Nuhu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button