Uncategorized

Manyan Mutanen Da Sukasa Baki Dan Ganin An Saki Hazikin Dan Sanda Mai Kishirin Arewa Da Nigeria Abba Kyari

Manyan Mutanen Da Sukasa Baki Dan Ganin An Saki Hazikin Dan Sanda Mai Kishirin Arewa Da Nigeria Abba Kyari

Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya bayar da belin tsohon shugaban bangaren ‘yan sanda masu kai ɗaukin gaugawa, Abba Kyari bayan ya shafe watanni 18 a tsare.

Kotun ta ce an bayar da belin ne kasancewar, dakataccen jami’in ɗansandan bai tsere daga gidan yarin Kuje ba a lokacin da aka kai hari gidan yarin a ranar 5 ga Yuli, 2022.

Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa, yadda Kyari da tawagarsa suka ki tserewa a lokacin da aka kai wa gidan yarin hari, inda kusan kashi 90 cikin 100 na fursunonin suka tsere, ya tabbatar da cewa Kyari a shirye yake ya fuskanci duk wani zargi da ake yi masa.

Alkalin ya ci gaba da cewa duk zargin da ake yi masa za a iya bayar da belinsa a kan su, kuma ba a tunanin cewa zai gudu.

An kama Abba Kyari tare da wasu ‘yan tawagarsa a watan Fabrairun 2022 bayan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta yi zargin cewa Kyari na da hannu cikin wasu miyagun kwayoyin da aka kama.

Rundunar ta IRT ta kama Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, a cikin watan Janairun 2022 bisa zargin su da safarar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 21.25, inda daga bisani suka mika waɗanda ake zargin ga hukumar NDLEA tare da hodar da aka kama su da ita.

An saki Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne daga gidan yari bayan sun gama fuskantar hukuncin da aka yanke musu.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare dakataccen ɗan sandan a kotun, Hamza Kyari, ya ce Abba Kyari ba zai iya komawa gida ba domin yana da wata tuhumar da zai amsa a gaban wani alkali a babban kotun tarayya da ke Abuja, inda har yanzu ake sauraron buƙatar belin da ya shigar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button