News

Masha Allah: Hukumar Yan Sanda Ta Kubutar da Mutum 58 Daga Hannun Yanbindiga

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce masu garkuwar da ɓarayin daji sun fara harbin tawagar jami’an tsaron a lokacin samamen da ‘yan sandan suka kai, abin da ya kai ga musayar wuta daga ɓangarorin biyu.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kuɓutar da mutum 58 da aka yi garkuwa da su a dajin Udulu na ƙaramar hukumar Gegu a jihar Kogi, wanda ya yi iyaka da dajin Sardauna na jihar Nasarawa.

‘Yan bindigar da suka fuskanci an fi ƙarfinsu sai suka tsere da harbi da dama a jikinsu, tare da barin mutanen da suka yi garkuwar da su.

Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja CP Haruna Garba ya ce za su ci gaba da aiki tuƙuru domin ceto duk wanda aka ji labarin an yi garkuwa da shi, tare da kama masu wannan aiki.

Sanarwar ta ce an samau nasarar ceto mutanen ne sakamakon haɗin giwwar ‘yan sanda da ‘yan sintiri da da mafarauta daga ƙauyuka daban-daban na Abuja, domin daƙile irin waɗannan laifuka da kuma kama masu aikata hakan don gabatar da su a gaban shari’a.

CP Haruna ya kuma buƙaci mutane da su sanya idanu tare da kai ƙorafin duk wasu mutanen da ba su yadda da sintirinsu ba, ta hanyar wasu lambobin waya da rundunar ta ware.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button