Kannywood News

Masu cewa mun Ki Yin Aure Idan Da Gaske Suke Su Fito Su Aure Mu – Fati Baffa Fagge

Masu cewa mun Ki Yin Aure Idan Da Gaske Suke Su Fito Su Aure Mu – Fati Baffa Fagge

Tsohuwar jarumar fim wadda tauraruwar ta ta yi haske a shekarun baya Fati Baffa Fagge, wadda aka fi sani da Fati Bararoji. Ta bayyana shirin ta na yin aure a duk lokacin da ta samu mijin da zai aure ta

Kamar yadda Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito, jarumar ta bayyana haka ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin jaridar adangane da rashin ganin ta da ba a yi tsawon lokaci a cikin harkar fim duk kuwa da cewar a shekarun baya Fati Baffa Fagge tana cikin jaruman da ake ji da su a cikin masana’antar, amma yanzu shiru an daina jin ta in da ta fara yin bayani kamar haka:

“To ka san komai yana da dalilin sa, tsawon lokacin da aka yi ba a gani na wasu matsaloli ne, kuma zan iya cewa ba matsaloli ba.

“Ka san ita rayuwa a koyaushe ana so a samu cigaba, duk da cewa harkar fim akwai cigaba, amma idan kana ciki, ya kamata ace ka samu wata hanyar kasuwanci wadda bayan fim akwai wani abu da mutum ke yi.

“To dalilin da ya sa kenan ba a gani na, don yanzu zan iya cewa na kai kusan shekara biyar ba a ganni a cikin fim ba.”

Ta kara da cewar: “Kuma ba a ganni ina shirya fim ba amma a duk lokacin da na samu dama don a yanzu ma haka akwai wasu finafinai guda biyu da nake son zanyi su nan da dan wani lokaci, don haka ban bar harkar fim gaba daya ba, duk abin da ake yi a cikin harkar fim ina shiga da ni ake yi kamar abin da ya shafi taro na ‘yan fim , ko biki na kawaye da sauran abokan arziki duk muna haduwa muna yi, saboda ka san mu ‘yan fim kan mu a hade yake.”

Da wakilin jaridar Dimokuradiyyar ya sake mata tambaya akan harkokin kasuwancin ta da kuma yadda za ta kwatanta rayuwarta ta baya da ta yanzu, sai jarumar ta ce:

“Harkar fim Allah yayi albarka a cikin ta, to kuma yanzu mun raba kafa, duk da cewar harkar fim ta na da wahala, ita ma harkar kasuwanci tana da wahala.

“Haka za ka sadaukar da rayuwar ka , ka hau jirgi ka tafi wata kasa , da fargaba da komai ka saro kaya ka zo ka sayar a nan kuma idan ka zo sayar da kayan ma ba sauki, don haka kowanne yana da na sa wahalar.”

Haka kuma da aka yi mata tambaya akan shirinta na yin aure jarumar ta ce:

“To aure lokaci ne, kuma a yanzu ina nan Ina shirin yi da yardar Allah idan na samu miji ko yanzu a shirye nake dana yi aure, don wasu sai ka ji suna cewa mun tsaya ruwan ido ne, kuma ba haka ba ne, in da gaske su ke yi su masu fadar su fito su gwada mana in har da gaske suna son su aure mu din, don haka duk wanda Allah ya kawo mini, ni zabin Allah nake nema wanda zai so ni ya girmama iyaye na kuma ya rike ni amana.”

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button