News

Matashin Daya Halaka mahaifiyarsa A Kano Ya Shiga Hannu

Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.

Rundura ƴan sanda a jihar Kano sun sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.

Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu’ammali da ƙwayoyi masu sa maye.

A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.

A jiya ne dai aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button