Kannywood News

Mawaki Ado Isa Gwanja Zai Angon Ce Da Maimuna Abubakar Wadda Akafi Sani Da Momee Gombe.

Mawaki Ado Isa Gwanja Zai Angon Ce Da Maimuna Abubakar Wadda Akafi Sani Da Momee Gombe.

Wani rahoto da ya karade shafukan sada zumuntar zamani shine, batun auren mawaki ado gwanja da momee gombe.

Tundai bayan mutuwar auren mawakin ake fuskantar wata kyakkyawar alaka na kulluwa tsakanin Ado Gwanja Da Momee Gombe.

Lamarin da wasu ke kallon wannan Alaka tasu da kamannin soyayya, inda suke zargin soyayya ce a tsakanin su.

To sai dai a yanzu magana tai nisa, domin har hoton kafin Aure wanda ake kira da Pree-weedding A Turanci Ya Fara Fita.

Duk da dai ba’aji daga bakin mutanen biyu ba amma ana kyautata zaton akwai wani abu dake shirin faruwa.

Andai Shaganin irin wadannan hotunan na jaruman kannywood na yawo mai kama da hoton aure.

Sai daga baya kuma suzo su baiyana cewa ba Aure zasuyi ba, fim ne ko kuma wata sabuwar waka zasu fitar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button