News

BIDIYO: ‘Yan Bindiga Sun Kama Barawon Dake Yi Masu Sace Sace, Sun Mika Ma Hukuma

BIDIYO: ‘Yan Bindiga Sun Kama Barawon Dake Yi Masu Sace Sace, Sun Mika Ma Hukuma

‘Yan bindiga sun kama barawon dake yi masu sace sace, sun mika ma hukuma.

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai ciki hadda bindigogi a kauyen Kilili dake karamar hukumar Safana na jihar Katsina sun kama wani matashi da suka ce barawo ne dake zuwa garin su da wasu muhimman gine-gine yana yi masu Barna tare da sace karafuna da sauran kayayyaki a gidajen su.

A wani bidiyo da wata jarida dake kafar sadarwar zaman ta Jino TV ta wallafa kuma Katsina Post ta samu, an ga yadda yan bindgar suka daure matashin mai suna Halliru wanda

ya ce shi dan kauyen Runka ne na karamar hukumar ta Safana, sannan suka gabatar dashi ga dan jarida domin ya mika shi ga jami’an tsaro.

Alh Usman Kachalla Rugga shine shugaban yan bndigar wanda ya shaidawa dan Jarida Usman Saleh Jino cewa dama sun dade suna neman kama masu zuwa suna yi masu sace-sace a gidajensu sai gashi yau Allah ya basu sa’a sun kama barawon.

Ya ce sunyi niyyar kashe shi to amma suka yanke shawarar gayyatar yan jarida cikin dajin domin nunawa Gwamnati irin kokarin da suke yi wajen kama bata gari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button