Kannywood News

Bidiyon Yadda Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale Ke Cigaba Da Kamfen A Kano

Bidiyon Yadda Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale Ke Cigaba Da Kamfen A Kano

Fitaccen Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale Ya Bude Wuta Wajen Yakin Neman Zaben Sa A Kano.

Jarumin Kannywood Abale Ya Cigaba Da Yakin neman kuri’un Al’umma A Takarar Da Yake Nema A Kano.

Jarumin Wanda Ya Tsaya A Matsayin Member Mai Wakiltar Kumbotso A Karkashin Jam’iyyar ADP.

Jarumin Na Cigaba Da Samun Goyan Baya Daga Masoyansa Yan Kallon Fina Finai. Ya Fita Kamfen Din Ne Tare Da Yan Uwan sa Jarumannan Kannywood.

Tabbas Takarar Da Jarumin Ya Tsaya Ta Girgiza Abokan Hamayya Na Jam’iyyu A Jahar Kano.

Inda Ta Baiwa Mutane Da Dama Mamaki, Sai Dai Ana Ganin Kamar Jarumin Da Dan Takarar Gwamnan Su Sha’aban Sharada Bai Zama Lallai Sukai Labari Ba.

Amma A Gefe Guda Kuma Wasu Na Ganin Zasu Iya Kaiwa Ga Nasara, Ganin Yadda Masoya Ke Cincirindo Da Dafifin Tarbar Su.

Daddy Hikima, Da Aminu Abubakar Alan Waka Da Mawaki Rarara Dakuma Mai Gayya Mai Aiki Sha’aban Sharada Ne Akan Gaba Wajen Kamfen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button