Kannywood News

Shekaru 14 Anan Nake Debowa Mahaifiyata Ruwa Saboda Itace Rijiya a…….

Shekaru 14 Anan Nake Debowa Mahaifiyata Ruwa Saboda Itace Rijiya a…….

Jaruma Rahama Sadau ta wallafa wadansu hotuna, inda ta nunawa masoyanta da mabiyan ta wata rijiya a kofar gidan mahaifiyarta, wacce a cewar ta; a cikin rijiyar ta ke diban ruwa, shekaru goma sha 4 da suka gabata.


Rahama sadau ta duki hotuna a kauyen da rijiyar take wato inda mahaifiyarta take zaune a da
A cikin yanayi na nishadi, jaruma Rahamar ta dauki hotunan a kauyen dake jihar Gombe wanda tace anan ne ta taso, kuma anan tayi kuruciya ita ta mahaifiyar tata.


Babban abin da ya baiwa wasu daga cikin mabiyan ta mamaki, shine yadda jaruma Rahamar ta dauki hotunan a garin kuma har ta yada su, tana mai ikirarin cewa ta dibi ruwa a wannan rijiyar shekara goma sha 4 baya.

Jarumai irinta suna jin kunyar bayyana bayan su saboda ..


Ba kasafai aka fiya ganin manyan taurari suna nuna wani abu da suka yi a baya ba, musamman idan na wahala ne amma ita tayi hoto ta wallafa, saboda yanzu sun sami daukaka, kuma idan suka bayyana bayan su, kamar za’a yi musu dariya ne, ko kuma suna ganin yanzu sun girmi wancan yanayin na baya.

Dalilin haka wadansu sukan nuna dama su daga babban matsayi suka taso, koda kuwa sun sha wahala a baya. Amma ita Rahamar hakan ko a jikin ta.

Daga gida ake fara samun tarbiyya, Inji Rahama Sadau
Sau da yawa akan ce wasu jaruman Kannywood suna yin wasu abubuwan da gayya don a dinga cece-kuce akansu wanda wasu ke ganin hakan ne kasuwancinsu.

Wasu na ganin idan har ba a maganar jaruman, kasuwarsu ta mutu. Hakan ke sa wani lokacin da kura ta lafa sai su kara taya da sabuwa bayan wani dan lokaci, Nishadiii blog taruwaito kukasance damu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button