![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/11/FB_IMG_1668894347283.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
Mawakin Hausa Ya Lakadawa Babarsa Dukan Tsiya A Tudun Wada Zariya
Wani Mawakin Hausa Hip-hop Ya Lakadawa Mahaifiyar Sa Dukan Tsiya A Zariya.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/11/FB_IMG_1668893396024.jpg?resize=300%2C229&ssl=1)
Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Yanzu Na Cewa, Wani Matashi Ya Lakadawa Mahaifiyar Sa Duka A Zariya.
Matashin Wanda Yanzu Haka Ke Hannun Yan Sanda A Zariyan Jahar Kaduna, Ana Cigaba Da Tsare Shi A Hannun Jami’ai
Matashin da ya zane mahaifiyarsa wanda ke hannun Ƴan Sanda Mai Suna Ali Boss ɗan tudun Wada Zariya Wanda Rahotanni Ke Cewa shine ya koyawa su 442 waƙa A Cewar Shafin Jaridar Alfijir Hausa Wanda Suka Wallafa A Shafin Su Na Facebook.
442 Wanda Yanzu Haka Shima Yake A Hannun Jami’ai A Jamhuriyar Nijar Bisa Karya Dokar Kasar.
442 Da Tawagarsa Sun Fada Hannun Hukumomi A Hannun Jami’an Kasar Bisa Zargin Leqen Asiri Dakuma Cin Amanar Kasa.
Laifin Da Ba Karamin Laifi Bane A Kasashen Duniya Baki Daya