News

Inna Lillahi! Matar nan da Mijinta ya kulle a daki mai suna Sadiya ta koma ga Allah

Inna Lillahi! Matar nan da Mijinta ya kulle a daki mai suna Sadiya ta koma ga Allah

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!

Matar nan da mijinta ya kulleta a daki me suna sadiya ta rasu.

Sedai an tabbatar mijin nata ya shiga hannun jami’an tsaro.

Sadiya din wadda labarin ta yayi matukar kada hantar mutane duba da irin zalincin da Mijin nata ya aikata Mata.

Daga It’z Kamalancy.

Ta tabbata daman dukkan mai rai mamaci ne muna rokon Allah yajikan ta yasa ta huta yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da Imani Amin.

Wani makusancin Mamaciyar ya wallafa a shafinsa kamar haka.

Innalillahi Wa’inna Ilaihirrajiun

Allah ya yiwa Sadiya Rasuwa.

Sadiya itace baiwar Allar da wani Azzalumin magidanci ya kulle ta a Daki yake bata hazbiya da koko da magunguna tare da mata wanda da wani ruwa mai wari.

Daga bisani mahifiyar ta taje ta Dauko ta ta dawo da ita nan Kano.

Adamu Abubakar Gwarzo Foundation -AAG-Foundation mun shiga jerin bada tallafin ganin an samo Mata lafiya amma cikin ikon Allah ta rasu.

Mahaifin ta ya rasu kwanaki kadan wanda Muna ganin yana da alaqa da halin da yaga yar sa a ciki.

Yanzu zamu dukufa wajen Nemo Mata hakkin ta wajen wannan mutum.

Ina Mika ta’aziyya ta ga yan uwanta da sauran abokan arziki Baki daya.

Allah ya gafarta Mata Amin.

Duk kungiyoyi da mutanen da suke neman tallafi da sunan wannan baiwar Allah, jama’a kuyi hattara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button