Religion

Bidiyon Da Dr. Idris Abdulaziz Bauchi Yaci Mutumcin Dr. Isa Ali Pantami Akan Minbarin Hudubar Juma’a

Bidiyon Da Dr. Idris Abdulaziz Bauchi Yaci Mutumcin Dr. Isa Ali Pantami Akan Minbarin Hudubar Juma’a

Akwai abun mamaki sosai yadda Dr. Idris Abdul’aziz Bauchi ya ci mutuncin Professor Isa Ali Pantami cikin rashin adalci don mu a ganin mu bai yi wa Pantami adalci ko kadan ba in de don TikTok ne.

Ai matsalar akwai lokacin shari’a wajen 2001 a na zafin maganan shari’a a arewa. An gayyaci Dr. Idris abdulaziz wa’azin sharia a Gombe da yaje. Anzo gabatar dashi yayi wa’azi wanda ya gabatar dashi shine pantami, pantami yace malam Dr. Idris yana wakiltar Dr. Hadi Dahiru bauchi ne daga bauch, shi Dr. Idris da ya fara wa’azi yace ba wakiltar Dr. Hadi Dahiru bauchi yake ba, shi ba wakilin dan bidia ba ne, hakan ya jawo rikici ya balle aka nemi kashe Dr. Idris dakyar yasha amma an soka masa wuka a kafa.

Wannan ya jawo yake ganin Dr. Isa pantami shi ya jawo aka yi masa wannan abu da ya faru a Gombe. Tun lokacin basa shirri kuma shine ainihin matsalar ba TikTok ba.

KAƊAN DAGA CIKI:

1- Ya kira Pantami da makaryaci karara yace “makaryaci”

2- Ya kira Pantami da cewa bashi da alaka da Addini harma cewa ya yi masu faɗin cewa haka basu san addini bane!

3- Hakanan ya nuna cewa duk tsare-tsarenda Pantami ya yi wahalar da mutane kawai ya yi musamman akan wannan harkar NIN

4- Yace tunda Pantami yaje wannan matsayi babu abunda ya tsinanawa musulunci in banda neman kuɗinsa da yake yi

Don akwai bukatar in zasu yi cecekuce su sauka daga mimbar su je gidan radiyo su yi maganganur su da tona wa juna asiri ba a mimbar ba.

Kuma a Gaskiya a nan bai kyauta wa Isa Pantami ba mu a ganin mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button