News

Tirqashi: Masarautun Kano Na Tangal Tangal Bayan Tafiyar Gwamna Ganduje

Masana Harkar tarihi da ke bibiyar al’amuran yau da kullum sun fara tofa albarkacin bakinsu kan dambarwar masarautun jihar Kano da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Biyo bayan kalaman da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya yi a wajen bikin ranar ma`aikata na kare matsayin gwamnatinsa game da matakin cire Sarki Muhammadu Sanusi na biyu.

Kazalika, da ƙirkirar sababbin masarautu a Kanon da suka haɗa da Bichi da Rano da Gaya da kuma Ƙaraye tare da tabbatar da ɗorewar su.

Wakilinmu  ya tuntubi Dr Shu’aib Shehu, wani masanin tarihi kuma darakta a cibiyar adana tarihin Arewacin Najeriya da ke gidan Sardauna, wato Arewa House, domin jin ra’ayinsa kan wannan batu.
Wanda ya ce komai ka iya faruwa, amma ba kasafai ake sauke sarki ya sake komawa kan karaga ba.

“Ba yau aka fara cire sarki a arewacin Najeriya ba, tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka zo suke cire sarakuna, su naɗa waɗanda suke so.

“Tun wannan lokacin ba a taɓa dawo da wani sarki ba saboda harkokin tsaro.

“Akwai sarakunan da aka cire su suka kai ƙara aka yanke hukuncin a dawo da su, amma ba a mayar da su ba, saboda zaman lafiyar al’umma, in ji Dr Shu’aib.
A lokacin wani jawabi da ya yi, a ranar bikin ma’aikata ta duniya, gwamna Abdullahi Ganduje ya ce masarautun Kano sun zo domin su zauna.

Kalaman gwamnan Kano dai ana musu kallon martani game da kalaman tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwanso.

Wanda a wata hira aka ji shi yana cewa watakila gwamnati mai jiran gado ta Abba Gida-gida za ta waiwayi maganar sauke Sarki Muhammdu Sanusi II.

Kwankwaso ya ce batun sake duba fasalin masarautun Kano na hannun sabon gwamnan Kano da zai kama aiki a watan Mayu.

Shi kuwa Gwamna Ganduje cewa ya yi “muna tabbatar muku waɗannan masarautu an yi su ne domin bayar da haɗin kai, domin ci gaba.

“Kuma ina tabbatar maku wannan masarautu dindindin, sun zauna zama da gindinsu, In Allah Ya yarda sai mahadi kature, kuma mahadin da zai ture Allah ba zai kawo shi ba, in ji Gwamnan Ganduje.

A yanzu haka muhawara na ci gaba da ƙara zafi tsakanin al’ummar masarautar ta Kano.

A ranar tara ga watan Maris na shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta bayar da sanarwar tsige sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi II.

A cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta jihar Kano ta ce dalilan da suka sanya ta tsige shi sun haɗa da rashin biyayya da kare mutuncin masarautar Kano da shigar da kansa cikin harkokin siyasa da kuma sukar gwamnati.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button