News

Tirqashi: Sulaiman Matashin Daya AurI Baturiya A Kano Ya Zama SOJA A Amurka

Matashin da ya auri baturiya yar shekara 46 a Kano ya zama soja a Amurka.

Wani matashi dan Kano mai suna Suleiman Isah da ya auri wata Ba’amurkiya, Janine Reimann ya shiga aikin sojan Amurka.

A tuna cewa a ranar 13 ga Disamba, 2020, Isah, wanda a lokacin yana da shekaru 23, ya auri Ms Reiman, mai shekaru 46.

An bayar da rahoton cewa, masoya biyu sun hadu a dandalin sada zumunta na Instagram watanni 10 kafin aurensu.

Reiman, mai sana’ar dafa abinci a Lindon, California, daga baya ta tashi zuwa Najeriya don bikin auren.

Daurin auren, wanda ya gudana a Masallacin Barikin Panshekara, ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.

Sai dai kuma Isah ya tabbatar da samun aikin sojan a yau Juma’a bayan bayan da ya wallafa hoton sa sanye da kakin sojojin Amurka a facebook hotonsa a shafinsa na Facebook.
Ya makala hoton tare da cewa, “Alhamdullillah- na gode”.

Don haka abokansa da masu fatan alheri sun mamaye sashin sharhi da sakonnin taya murna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button