News

Wata Sabuwa: Shugaban Yan Bindigar Jahar Zamfara Bello Turji Yana Nan A Raye Tare Da Sabuwar Daba

Wata Sabuwa: Shugabaan Yan Bindigar Jahar Zamfara Bello Turji Yana Nan A Raye Tare Da Sabuwar Daba

Kamar yadda zaku gani a hoto, Bello Turji yana zaune a kan kujera cikin kakin ‘yan sanda, ga bindigar RPG jingine jikin bishiya ta bayansa, sannan ga sauran mayakansa wasu a cikin kakin sojoji tare da sauran jama’arsu da matansu suna zaune cikin izza.

Kuma dai har yanzu Bello Turji yana rike da wasu kauyuka suna karkashin ikonsa a jihar Zamfara da Sokoto, musamman kauyukan Gusami da Gora wanda suke karamar hukumar Birnin Magaji jihar Zamfara

Duk wanda yayi nazarin wadannan hotuna ya kallesu da kyau yaga irin makamai da abin hawa da suke gurin barayin zai fahimci cewa mutanen nan suna samun taimako da daurin gindi daga gurin manyan maciya amanar tsaron Nigeria da miyagun ‘yan siyasa

Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen ‘yan ta’adda da maciya amanar tsaron Nigeria

Arewa Intelligence
1-1-2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button