Kannywood News

Yadda Jaruma Fati Kk Tayi Aure A Asirce Batare Da Sanin Abokan Sana’ar ta ba

Bikin Jaruma Fati Kk Wanda Akayi A Asirce
Hoton Bikin Jaruma fati kk Jarumar Da Akai Bikinta A Asirce Batare Da Abokan Sanaarta Sun Sani ba.

Fitacciyar Jarumar Shirya Fina Finan Hausa A Kannywood A Kwanakin Baya Mai Suna Fati Kk Tayi Aure A Asirce Batare Da Sanin Abokan Sana’arta Ko Yan Media Ba.

Wata Sabuwar Al’ada Da Jaruman Kannywood Mata Suke Yawan Amfani Da Ita A Yanzu Shine. Boye Shirin Auren Su Dakuma Wanda Zasu Aura Din Ga Abokan Sana’ar Su Da Kafafen Sada Zumunta. Sai Dai Kawai Aji Cewa An Daura Auren Inda Wasuma Daga Cikin Jaruman Sai Dai Kawai Adaina Ganin Su A Masana’antar. Wanda Ko Labarin Auren Nasu Ma Babu Mai Sani Sai Dai In Anyi Bincike Daga Baya A Gano Cewar Aure Sukai.

Wajen Shagalin Bikin Da Akai Na Jarumar
Wajen Shagalin Bikin Jarumar Da Akai

Irin Hakan Ce Dai Ta Faru Ga Jaruma Fati Kk Wadda Tai Aure A Jiya Juma’a 12-2-2021 batare Da Kowa Yasan Shirin Auren Na Jarumar Ba.

Inda Sai Dai Kawai Gani Akai Tana Wallafa Hotuna Da Bidiyon Bikin Nata Gami Da Rubuta Cewa Allah Ya Bata Zaman Lafiya Da Mijinta.

Addu’ar Da Jarumar Tayiwa Kanta Bayan Daura Auren. Da Nufin Sanar Da Abokan Sana’ar tata.

Fati kk dai ta tabayin aure a kaduna Daga Bisani ta Fito Da Yaya Biyu. Wanda Ta Bayyana A Wata Hira Da Tai Da Manema Labarai Cewa Rashin Jin Dadin Zama Da Ahlin Mijinta Ne Dalilin Mutuwar Auren Nata. Wanda Wannan Na Daya Daga Cikin Kaalubalen Da Jaruman Kannywood Mata Ke Fuskanta A Gidajen Auren Su.

A Yanzu Haka Dai Babu Wanda Yasan Wanene Mijin? Ina Za’a Kaita Da Dai Sauran Alamura Da Suka Shafi Bikin Wanda Ko Abokan Sana’arta Dake Tayata Murna Da Bikin Basu Da Masaniya Akan Auren.

Amarya Fati kk

Zadai Mu Iya Cewa Wannan Boye Batun Auren Nada Nasaba Da Shirye Shiryen Aure Da Dama Da Muka Dinga Ji A Media Amma Kafin Rana Tazo Sai Labari Ya Sauya Wanda Ake Kyautata Zato Suka Ake Kaiwa Da Zuga Ga Dangin Mijin Da Zai Auri Yar Film Din Wanda Hakan Yasa Mafi Akasari Sai Dai Kawai Aji Sunyi Aure.

Muna Taya Amarya Fati Kk Murna Da Addu’ar Allah Ya Bata Zaman Lafiya Da Mijinta Masu Burin Aure Anan Gaba Allah Ya Basu Abokan Zama Na Gari.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button