News

Za’a Kafa yansandan Jihohi cool 1

Za’a Kafa yansandan Jihohi

Gwamnonin Babbar Jam’yar adawane suka baiyana Hakan a wurin wani taro da suka yi a ranar Litinin a Abuja, babban birnin taraiyar Nigeria.

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi kira da a kafa rundunonin ƴansanda na jihohi a karkashin wata doka da zata hana yin katsalandan daga duka matakan gwamnati.

Taron ya kuma tattauna yanayin da ƙasar ta tsinci kanta game da wahalhulun da mutane ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kuma tsaro.

Read also

Gwamnonin na PDP sun kuma sha alwashin ci gaba da taka rawar da ta dace domin samar da tsaro ga al’ummansu, abun da a cewarsu ya sa suka jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha.

Inda suka buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen ɓullo da wasu shirye-shirye da za su haɗa da duka ɓangarorin gwamnati don samar da mafita mai ɗorewa.

Yansandan
Yansandan

Taron ya kuma koka kan karyewar darajar kudin ƙasar wato naira, inda suka nemi hukumomin da abun ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.

Sai dai jihar Zamfara da ta Filato na daga cikin jihohin da jam’iyyar ta PDP ke mulki, kuma suke kan gaba wajen fuskantar matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a tsawon shekaru.

Lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da ta dukiyoyi.

Visit our Facebook

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button