News

Ƴan bindiga sun kashe wani ɗalibin jami’ar BUK da ya gama da sakamako mai daraja ta ɗaya

Ƴan bindiga sun kashe ɗalibin BUK da ya gama da sakamako mai daraja ta ɗaya

Wasu ƴan bindiga sun kashe Sule Mathew, wanda ya kammala karatu a fannin sadarwa da sakamako mai daraja ta ɗaya a Jami’ar Bayero Kano, BUK, kuma ya yi horon sanin makamar aiki a PRNigeria.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ƴan bindigar sun kashe Mathew ne a yayinda yanke tafiya zuwa Jihar Anambra tare da sauran fasinjoji.

An kashe Mathew ne tare da sauran fasinjoji a Ekwulobia, ɗaya da ga cikin manyan biranen Jihar Anambra bayan Awka, Onitsha da Nnewi.

Abokan karatunsa da ƴan uwansa sun ce ya na kan hanyarsa ne tare da wasu fasinjojin sai yan bindigar su ka tare su, su ka kuma kwantar da su sannan suka zuba musu harsashi har sai da dukkan su su ka rasu.

Sun ce a lokacin da ya tafi, a na ta korar wayar sa ba ta shiga, sai da ga baya su ka samu wannan mummunan labari.

An ce an kai gwarwakin na su asibitin Ekwulobia.

Wani abokin karatun Mathew ɗin ya ce a na daf da kiran su zuwa shiga sansanin horon ƴan bautawa ƙasa sai wannan ibtila’in ya faɗa masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button