News

Ƴan ta’adda sun hallaka wasu a wajen shaƙata wa a Gaidam

Ƴan ta’adda sun hallaka wasu a wajen shaƙata wa a Gaidam

Ƴan ta’adda da a ke zargin ƴan ISWAP ne ko Boko Haram, sun hallaka wasu masu yawon shakata wa a Ƙaramar Hukumar Gaidam da ke Jihar Yobe.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa ƴan ta’addan sun saci jiki sun shiga garin, inda su ka dira a wata mashaya, inda a ke sayar da giya da naman kare.

A wani sako na kada sojoji su gan su, sai yan ta’addan su ka ɗaure waɗanda abin ya shafa su ka kuma yi musu yankan rago.

Wasu majiyoyi sun shaida wa PRNigeria cewa wasu ma an cire musu kan nasu ɗungurungum an kuma ɗaora shi a kan kirjin su

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button