News

Babban Aboki Ya Kashe Abokinsa Kuma Ya tsere Da Motarsa Da Naira Miliyan Biyu

Babban aboki ya kashe abokinsa kuma ya tsere da motarsa da naira miliyan biyu

Wani matashi mai shekara 25 mai suna Bashir Ibrahim ya daba wa wani abokinsa wuka a Minna babban birnin jihar Neja, kuma ya tsere da motarsa da kudi naira miliyan biyu.

Bashir ne babban abokin mamacin yayin da yayi aure ‘yan watannin da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Bashir ya gayyaci mamacin ne mai shekara 28 da haihuwa zuwa unguwar Tudun Fulani ta birnin Minna kimanin mako biyu da ya gabata domin su tattauna kan wata damar kasuwanci da ta bayyana a cewarsa.

Sai dai Bashir ya daba wa amamacin wuka bayan da ya isa wurin, kuma ya tsere da motarsa kirar Peugeot 206 da kuma naira miliyan biyu da ke cikin motar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar ta Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin ta hannun kakakinta DSP Wasiu Abiodu, wanda yace bincike ya sa sun kama Bashir da wani wanda ya taimaka masa mai suna Aliyu Ibrahim wanda ke da shekara 22 da haihuwa.

Akwai kuma wani Suleiman Mahmud da shi ma ake tuhuma da hannu wajen aikata wannan aika-aikar, wanda tuni ya tsere, sai dai ‘yan sanda na ci gaba da nemansa.

Jaridar ta kuma ce Bashir ya tsere da motar ne zuwa Kano domin ya sayo wasu sinadarai da ake wanke zinare da su da kudin mamacin.

Sai dai bayan ya koma Minna ne ‘yan sanda suka damke shi a wani otel da ke kan babbar hanyar Wetern Bypass a Minna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button