Religion

Matasan Kiristoci Sun Saya Wa Masallaci Sabon Janareta A Jihar Filato

Matasan Kiristoci Sun Saya Wa Masallaci Sabon Janareta A Jihar Filato

Wasu Matasan Kiristoci sun saya wa Masallacin Juma’a na garin Gana Ropp da ke Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato sabon injin Janareta domin samar da hasken lantarki a masallacin.

Masallacin dai majiyarmu ta ce ya sha fama da matsalar lantarki saboda rashin sahihin injin janareta.

“Ko Tafseer za yi sai an yi Aron Inji, hatta Sallar Juma’a sai an yi aron Injin, Masallacin ya kai A kalla shekaru 3 yana fama da wannan matsalar. Sai gashi da yammacin Juma’ar nan wannan matasa sun gwangwaje Masallacin Da Sabon Generator na Kimanin Kudi Naira dubu ɗari da sittin da biyar (165,000).”

“Allah ya saka musu da alkhairi. Allah ya ƙaro mana zaman lafiya a Jihar Filato amin.” In ji majiyar tamu.

Wannan dai alama ce ta ƙoƙarin da ake yi na maido da dawwamammen zaman lafiya a jihar ta Filato mai fama da rikicin addini da ƙabilanci ya fara haifar da ɗa mai ido.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button