News

Ɗan shekara Goma Sha Hudu 14 ya mutu a ruwa a Kano

Ɗan shekara 14 ya mutu a ruwa a Kano

Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro ɗan shekara 14, Musa Sani a wani ruwa mai suna Rafin Mukugara da ke ƙauyen Kumbagawa a Ƙaramar Hukumar Karaye.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar a yau a Kano, ya ce lamarin ya faru a jiya Juma’a da safe.

Ya ce hukumar ta karɓi rahoto na gaggawa a ofishinta da ke Karaye da ga wani Abdulbaki Abubakar da misalin ƙarfe 8 na safe, inda ya ce nan take hukumar ta tura jami’an ta su ka je wajen da misalin ƙarfe 8:05.

Ya ce an fito da yaron da ga cikin ruwan cikin halin rai-kokwai-mutu-kokwai, inda da ga bisani a ka tabbatar da cewa ya rasu.

Abdullahi ya ƙara da cewa tuni a ka miƙa gawar mamacin ga Dagacin Karaye, Suraja Magaji.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button