Politics

Abin Da Ya Sa Na Zama Mawaƙin Siyasa Sabanin Mawakin Yabon Annabi – Bashir Ɗandago

Abin Da Ya Sa Na Zama Mawaƙin Siyasa Sabanin Mawakin Yabon Annabi – Bashir Ɗandago

SHAHARARREN mawaƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.) ɗin nan, Malam Bashir Ɗandago ya bayyana dalilin da ya sa shi ma ya bi sahun mawaƙan siyasa, saɓanin yadda aka san shi tsawon shekaru.

Ko da yake a wasu lokutan ya na yin wasu waƙoƙin na faɗakarwa ko na jama’a ko sarakuna, kamar waƙar da ya yi wa Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero, amma dai da sunan siyasa ba a taɓa ji ya yi ba.

A ‘yan kwanakin nan sabuwar waƙar da sha’irin ya yi wa jam’iyyar NNPP da ɗan takarar ta na shugaban ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ta cika garin Kano, wanda hakan ya tabbatar da cewa shi ma ya zama mawaƙin siyasa.

Mujallar Fim ta tattauna da Bashir Ɗandago a game da shigar sa siyasa da kuma waƙar da ya yi, inda ya ke cewa: “Gaskiya ne na yi waƙar siyasa wadda na yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma jam’iyyar NNPP duk da cewa a baya ban taɓa yi ba, domin ni tun da na ke ban taɓa waƙar siyasa ba sai a wannan lokacin.”

A game da dalilin sa na shiga waƙar siyasa kuwa cewa, ya yi, “To, an kai mu bango ne shi ya sa mu ma mu ka fito domin mu yi tamu siyasar. Domin yanzu idan ka duba kowane shehi ya na yin siyasa kuma ya na da ra’ayin sa a siyasar. To amma kowa idan ya samo daga shi sai ‘ya’yan sa, don haka ni ma na ga ina da damar da zan fito na yi tawa siyasar ba tare da na jingina da wani shehi wanda idan ya samu daga shi sai ‘ya’yan sa ba.

“Don haka ni ma siyasa ta na ke yi ta ƙashin kai na, kuma zaɓi jam’iyyar NNPP da ɗan takarar ta Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin zaɓin da ya kwanta mini, don haka ni shi na ke yi. Ba zan tsaya ina jingine da wani ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button