News

ABIN TAKAICI: Tsagerun Kudu Sun Kone Mota Makare Da Shanu Wadda Ta Taso Daga Arewa

ABIN TAKAICI: Tsagerun Kudu Sun Kone Mota Makare Da Shanu Wadda Ta Taso Daga Arewa

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsageu sun tare motar jama’ar da suka taso daga jihar Taraba, sun kone ta kurmus Rahoton ya bayyana cewa.

An kone shanu, wasu sun tsere daji yayin da mutanen da ke cikin motar suka tsallake rijiya da baya Lamarin da bai kasance na farko ba.

An sha samun irin wannan barna daga ‘yan ta’adda a yakin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata mota makare da shanu akan titin Ezinifitte/Uga a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inji rahoton jaridar Punch.

A cewar wata majiya, motar tana kan hanyarta ta zuwa wata kasuwa a jihar ne, inda aka samu akasi ‘yan bindigar suka kai hari tare da kona ta.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, wani ganau ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da ke cikin motar sun samu raunuka, inji rahoton Punch

Wani faifan bidiyo na lamarin da aka gani a kafafen sanda ya nuna yadda wasu shanun suka watse daga hanyar zuwa cikin dazukan da ke kewaye. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ceto wani Mohammed Lawan na jihar Taraba tare da dawo da dabbobi 34 a hanyar Ezinifite da Uga a karamar hukumar Aguata. An yi aikin ceton ne biyo bayan kiran gaggawa da aka yi a yau, 8 ga watan Mayu, da misalin karfe 8 na safe, na kone-kone da kuma cin zarafin dabbobi da ‘yan bindiga suka yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button