News

Abinda Sheikh Ali Isa Pantimi Ya Fadawa Iyayen Hanifa Da Yaje Ta’aziyar Rasuwar Hanifa.

Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Yakai Ziyara Gidan Su Marigaya Hanifa Abubakar Kano

Abinda Sheikh Ali Isa Pantimi Ya Fadawa Iyayen Hanifa Da Yaje Ta’aziyar Rasuwar Hanifa.

Malam Isa Ali Pantami ya samu kai ziyara Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar wanda aka kama shugaban makarantarsu kan laifin kisan ta.

Farfesa Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, sannan mahaifin yarinyar ya jagoranci shiga cikin gida in da ya yi ma mahaifiyar da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi.

Malam Ya yi nasiha ga iyayen yarinya mai albarka, akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan.

Professor Isa Ali Pantami ya roki Allah Ya sanya Marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta.

Ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.

Iyayen sun yi godiya ga Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.

Allah Ya kiyaye na gaba.

https://youtu.be/GOMOfSDjPIA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button