News

Abinda Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Yayinda Na Daga Bindiga Zan Harbesa: Barawon Soja

Abinda Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Yayinda Na Daga Bindiga Zan Harbesa: Barawon Soja

Sojan da ya kashe babban Malamin Addinin Musulimcia A jihar Yobe ya bayyana abinda Sheikh Goni Aisamu ya fada masa yayinda ya daga bindiga zai harbesa.

Hukumar yan sanda ta bayyana sakamakon bincikenta kan Sojojin da akewa zargin kisan Sheihk Goni Aisami.

An yi jana’izar Shehin Malamin mazauni jihar Yobe ranar Asabar kuma dubban mutane sun hallara A Wajen Jana’izar

Lance Kofur John Gabriel ya bayyana yadda ya yaudari Sheik Goni Aisami-Gashua, kafin harbinsa da bindiga har lahira a kan titin Gashua- Jaja Maji.

Yayinda yake jawabi lokacin da yan sanda suka gabatar da shi gaban yan jarida ranar Laraba, Kofur John ya ce babban Malamin ya yi masa tambayoyi biyu yayinda yake kokarin kashe shi.

Rahoton DailyTrust. Yace: “Yayinda muka kusa Jaji-Maji kuma tagogin motar na sauke, sai na fada masa ina jin kara karkashin motarsa, sai yace shima yana ganin akwai wani abu.”

“Sai ya faka motar. Yayinda ya tsaya a gefen hanya ya fita daga motar, sai na bi sa.

Bayan ya gama dubawa bai ga komai ba.” “Ni kuma tuni na fito da bindiga da harsashi lokacin da yake duba motar.

Da bai ga komai ba, sai na nuna masa bindiga, sai ya tambayeni, ‘Me na maka?” Ni kuma na bashi amsa, babu abinda kayi min.”

“Sai ya sake tambaya na, ‘Kana son ka kashe ni ne?’ Sai na nace masa Bana son kashe ka’ Sai yayi shiru.

Sai na harba bindiga don tsoratar da shi ina tunanin zai gudu. Amma bai gudu ba, sai ya shiga cikin motar, sai na bindigeshi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button