Uncategorized

Addinin Mu Ba Abin Wasa Bane, Malamai Sun Fara Mayarwa Da Davido Martani Kan Wakar Batanci

Addinin Mu Ba Abin Wasa Bane, Malamai Sun Fara Mayarwa Da Davido Martani Kan Wakar Batanci

Ajiyane wannan sanannen mawakin kudancin kasar nan me suna davido yasaki wata sabuwar waka a shafinshi na twiter wanda wani yaro mesuna olamilekan emeka taiwon ya rera kuma ya hau fefan videon

• Acikin videon shi mawakin ya hau kan saman masallaci ra raba kafa akan sifikar masallaci yana waka akasa kuma yan rawar tashi sunyi shigar musulunci da jallabiya sunyi sahun sallah dasu da liman din duka suna sallah suna tikar rawa.

Da yake mayar da martani kan bidiyon Da Davido Yayi,

Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan Sadarwa ta zamani ya wallafa a Twitter cewa.

Wannan abun kwata-kwata rashin mutunci, cutarwa da kuma cin zarafi @davido. Na dauka duk kun san cewa mu Musulmi ba mu hada addininmu da barkwanci ta kowace fuska ba, musamman Salah (sallah), wanda tsarki ne kuma na biyu daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.

“A cikin Salah, Musulmai suna tuna da Ubangijinmu, Allah, suna bayyana kaunarmu da girmama shi kuma suna kira da kokarin nuna godiyarmu a gare Shi.

• Wannan izgili ne ga addinin musulunci dakuma cin fuska agaremu mu musulmi. Muna addu’a Allah ya la’anci davido da wannan yaron Allah ya durkusar dasu har kasa. Muna kuma kara kira da hukumomi dasu dakatar da abubuwa makamantan wannan dan gudun rikicin Addinai.

Allah ka daukaka musulinci da musulmai
Ka kaskantar da kafirci da kafirai 🙏.

Credit: Bagadaza Ameenu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button