entertainment

Tsohon Mai Taimaka Wa Buhari, Bashir Ahmad, Ya Ya Kalubalanci Davido Kan Yin Wakar Batanci Ga Addinin Musulunci

Tsohon Mai Taimaka Wa Buhari, Bashir Ahmad, Ya Ya Kalubalanci Davido Kan Yin Wakar Batanci Ga Addinin Musulunci

Tsohon mai taimaka wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya caccaki shahararren mawakin nan na Najeriya, Davido kan wani rubutu da ta yi kwanan nan a shafin twitter.

tsohon mai taimaka wa, Bashir Ahmad, na tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya caccaki shahararren mawakin nan na Najeriya, Davido game da wani rubutu da ya yi kwanan nan ta shafinsa na Twitter yana sanar da sabuwar wakar da zai saki ta batanci ga musulmai.

Mawaƙin ya rubuta a cikin rubutun Cikin harshen Turanci cewa, “ina mai sake gabatar da @logosolori tare da sabuwar wakar mu mai suna ‘Jaye Lo’. Burin mu shine lokaci daya! Mu karbi duniya! Wakar ta zaga Ko’ina.

Sakon na tweet ya samu rakiyar wani bidiyo na yaron da yaiwa signee zaune a kan wani ginin masallaci.

A farko-farko na bidiyon an ga mutane sanye da jallabiyya suna sallah a harabar masallaci.

Da yake mayar da martani kan bidiyon, Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan Sadarwa ta zamani ya wallafa a Twitter cewa,

“Akwai dalilai da yawa da suka sa kowane Musulmi yake kallon hakan a matsayin batanci ga addinin musulimci da musulmai. wannan abun kwata-kwata rashin mutunci, cutarwa da kuma cin zarafi @davido. Na dauka duk kun san cewa mu Musulmi ba mu hada addininmu da barkwanci ta kowace fuska ba, musamman Salah (sallah), wanda tsarki ne kuma na biyu daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.

“A cikin Salah, Musulmai suna tuna da Ubangijinmu, Allah, suna bayyana kaunarmu da girmama shi kuma suna kira da kokarin nuna godiyarmu a gare Shi.

Yin Salah yana hada mutum fuska-da-fuska da Allah. Wannan shi ne abin da muka yi imani da shi, kuma wannan shi ne bangaskiyarmu.

Da fatan za a girmama shi. Babu wani musulmi da zai same shi a matsayin girmamawa ko karbuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button