entertainment

GABA DAI GABA DAI ISLAMA: Davido Yaji Wuta Ya Goge Wakar Batanci Tare Neman Yafiya Ga Al’ummar Musulmai.

GABA DAI GABA DAI ISLAMA: Davido Yaji Wuta Ya Goge Wakar Batanci Tare Neman Yafiya Ga Al’ummar Musulmai.

Fitaccen Mawakin Kudancin Nigeria Davido, Ya Goge Wakar Da Yayi Tare Neman Yafiyar Al’ummar Musulmi.

Tun Bayan Kiraye Kiraye Da Yai Yawa Daga Bangarori Da Dama, Kan Batun Wakar Da Ake Zargi Ta Batanci Ga Musulmai.

Wani Matashi Mai Suna Abdul’aziz Ya Wallafa A Shafin Na Facebook Cewa.

Maganar Allah shine idan Davido yana da laifi a wannan lamarin to bai wuce kaso 1 cikin dubu ba. Shi ba musulmi bane, saboda haka ba lallai ya san matsayar musulunci akan abubuwa ba.

Shi Davido taka sawun barawo ya yi. Wani ne da ake wa lakabi da Logos Olori, wanda an ce Musulmi ne, ya yi waka ya saka ta a twitter shi kuma Davido ya yi sharing. Da kuma ya ga ana cece-kuce ya goge retweet din.

Ina kyakkyawan zaton shi kansa wanda ya yi wakar da kyakkyawar zuciya ya yi ta don nuna muhimmancin addininsa a wurinsa. Shi ma kuma Davido ina kyautata tsammanin da kyakkyawar zuciya ya yi sharing saboda nuna cewa bambancin addini ba wani abu bane a wurinsa.

Wannan abu ne kawai da ya kamata a nuna musu cewa ba haka addininmu yake ba sai a wuce wurin. Amma ba wai zage-zage da tsine-tsine ba.

Fahimta ta kenan. In ka ji haushi ka yi hakuri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button