entertainmentKannywood NewsTrending

Ahmed Musa Yayi Wa Magoya Bayansa Wasu Adduoi Na Musamman Bayan Dawowarsa Daga Masallaci

 

 

 

Shahararren Tsohon Dan Wasan Kwallon Kafar Kano Pillars Kuma Kaftin Din Super eagles Ahmad Musa.

ya nuna Wasu Manyan motocin alfarma Da Aka Ajje A garejinsa Wanda Kudaden Motocin Ya Haurewa N200m yayin da Dan Wasan Ya Shirya Domin Tafiya masallaci Da Nufin Yin Ibadar Sallar Juma’a

Ahmad Musa Hoton Ranar Juma’a

 

A Wani Sabon Hoto Da Ya wallafa A Shafinsa Na Instagram, matashin mai shekaru 28 ya yi addu’o’i domin karfafa wa masoyansa gwiwa Kafin Tafiyar sa Izuwa Masallaci Domin Gudanar Da Sallar Juma’ah

Ahmad Musa A Daki Mai Tsarki

 

A matsayinsa na jajirtaccen Musulmi, Mai Gudanar Da Ibadarsa Akan Lokaci Matashin Sannan Mai Yawaita Addu’a Akan Duk Wani Lamari Da Ya Shige Mai Duhu.

A Yauma Dan Wasan Yayi Wasu Muhimman Adduoi A Shafinsa Na Instagram Kamar Yadda Yadda Yasa Yi Lokaci Zuwa Lokaci Musamman Ma A Rana Irin Ta Juma’a

Ahmad Musa Ranar Jumaa a gidan sa

 

Ahmad Musa Ya Fara Addu’ar ne Kamar Haka.

Ya “Allah Madaukakin Sarki Muna Rokonka Da kar Ka taba bari zuciyarmu ta rikice da jarabawar rayuwa.

Ya “Allah Muna Roko Ka ci gaba da bude mana kofofin Rahamarka, Ka saukaka hanyoyinmu, ya karbi ibadunmu, Ka albarkaci karshenmu, Ka sanyaya kaburburanmu, ka gafarta mana zunubanmu da na iyayenmu kuma daga karshe ka Kasa Jannatul Firdaus Ya Zama gidanmu na karshe Ameen. Jummat Mubarak. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button