![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/09/FB_IMG_1662385221740.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
Allah Sarki: Ku Kalli Yadda ‘Yan bindiga suka mayar da mutanen Zamfara bayi bayan sace su a Masallacin Juma’a
Rahotanni daga jihar Zamfara ta Najeriya na cewa, ‘yan bindiga sun mayar da mutane 44 da suka sace a Masallacin Jumu’a bayin dole, inda suke yi musu noma a gonarsu ta gero da dawa.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/09/FB_IMG_1662384052684.jpg?resize=300%2C181&ssl=1)
‘Yan bindigar sun kira ‘yan uwan mutanen ta wayar tarho, inda suka shaida musu cewa, yanzu haka suna nan suna yi musu noma, amma kawo yanzu ba su bukaci a biya su kudin fansa ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne ‘yan bindigar suka sace masu ibadar daga babban Masallacin Juma’ar garin Zugu da ke Karamar Hukumar Bukkuyum a jihar ta Zamfara.
Mazauna garin sun ce, ‘yan bindigar sun boye bindigoginsu a cikin tufafinsu kafin su yi wa masu ibadar dirar mikiya a daidai lokacin da babban limami ke gab da fara gabatar da huduba.
Jim kadan da shiga cikin Masallacin ne, ‘yan ta’addar suka fito da bindigoginsu tare da yin harbe-harbe.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, tuni ta fara farautar wadannan ‘yan bindigar domin ceto Masallatan daga hannunsu.