News

Allahu akbar – Mahaddacin Al-Qur’ani Alaramma Abdulrahman Bello Ya rasu sakamakon bigeshi da Mota tayi

Allahu akbar – Mahaddacin Al-Qur’ani Alaramma Abdulrahman Bello Ya rasu sakamakon bigeshi da Mota tayi

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
Alaramma Abdurrahman Bello mahaddacin Al Qurani ya rasu. Allah ya karbi abinshi sakamakon mota da ta buge shi.

Kafin rasuwarsa margayi Abdulrahman shine Babban dan Barista Bello Zubairu, Mai tsawatarwa na majalisar dokokin jahar Kaduna.

Muryoyi ta ruwaito marigayi Abdulrahman Matashine mutumin kirki mahaddacin Al-Qur’ani mai biyayya ga iyayen sa dana gaba dashi, Hakiƙa anyi rashi babba, Allah yajiƙan sa yayimasa rahma ya haskaka makwancin sa da sauran mamatanmu musulmi.
Allah ubangiji yaji kansa da Rahama yasa aljanna makomarsa Amin.

Innalillahi Wa’ina Ilaihir Raji’un.

Anyi Jana’izar Babban yaron Barrister Bello Zubairu Clark na majalisar dokokin jahar Kaduna Marigayi Alaramma Abdulrahman Bello kamar yadda addinin musulunci yatanadar.

Mai Girma Speaker KADSHA Rt Hon Yusuf Ibrahim Zailani tare da Shugaban Karamar Hukumar Igabi Hon Jabir Khamis Rigasa sun samu damar halarta Jana’izar, Muna Addu’a Allah madaukakin sarki yajiqan sa yayi masa rahma.🙏🙏🙏

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button